Yayin da ake kai ruwa rana game da samarwa makiyaya wurin kiwo a cikin jihohin Najeriya, Gwamnan jihar Ekiti Ayodele Fayose yace dokar da ya kafa na hana kiwo barkatai nan nan daram.
Gwammnan ya furta hakan ne sailin da yake tattaunawa da wakilin sashen Hausa na Muryar Amurka, Hassan Umaru Tambuwal ta wayar tarho.
Fayose yace daya daga cikin abinda yayi game da wannan dokar shine ya tabbatar kowa nada rawar da zai taka game da wannan dokar, domin samun nasarar taga kowa da kowa.
Yace ya kafa dokar ce ba tare da jiran sai wani ko wasu sun mutu ba kafin ace a samar da doka, kuma wannan dokar ba anyi ta bane domin wasu rukunin jamaa sai domin masu aikata ayyukan assha koda kuwa da wani irin harshe suke magana.
Ga Hassan Umaru Tambuwal da karin bayani: 3’37.
Your browser doesn’t support HTML5
Gwamnan Jihar Ekitin Ayo Fayose Yace Dokar Hana Kiwo ba Gudu Baja Da Baya.