Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matasa A Garin Zing Cikin Jihar Taraba Sun Kona Caji Ofis


Matasa a garin Zing a cikin jihar Taraba sun kona caji ofis yayin wata zanga-zanga dasuka yi

Shi dai wannan sabon yamutsin ya barke ne bayan da wasu gungun matasa daga wani kauye na Zing suka yi wata zanga-zangar neman a basu wasu mutane uku da yan sanda suka kama.

Su dai matanen an kama su ne bisa zargin kisan wani dan Achaba da aka samu gawarsa a kauyen Dogwe,to amma kuma sai yan sandan suka ki.

Ganin haka ne sai masu zanga-zangar suka soma daukar doka a hannunsu, inda suka soma fashe-fashe da kone-kone da ta kai sun kona babban ofishin yan sanda dake garin na Zing.

Ko baya ga kona caji ofis din sun saki wasu dake hannun yan sanda, ko da yake kawo yanzu ba’a tabbatar da ko sun sulale da makamai ba ko kuma a’a.

Wasu mazauna garin da aka tattauna dasu ta waya sunce yanzu haka an turo karin jami’an tsaro zuwa yankin don tabbatar da doka da oda.

Ga Ibrahim Abdulazeez da Karin bayani 2’45:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:45 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG