Gwamnatin Buhari Zata Tabbatar da Mulki Mai Adalci da Bin Kaida Kain da Nain

Shugaban Najeriya Muhammad Buhari

Bayan da aka yi mashi kyakyawar gabatarwa shugaba Buhari ya godewa gwamnatin Amurka da tattaunawa mai ma'ana dayayi fatan cewa kasashen biyu sun karfafa dangantakar dake tsakaninsu

“Yace kasancewar manyan ‘yan kasuwan Amurka a wurin babu shakka nuni ne cewa akwai kwakwarar dangantaka tsakanin Amurka da Najeriya kuma dangantaka ce dake cigaba”. Shugaba Buhari ya yabawa kungiyar da tara shugabannin kamfanonin Amurka wadanda suka bayyana masa shirinsu da kuma abubuwan da suke yi da kasarsa.

Yace nufinsa a taron shi ne ya bayyana masu inda kasarsa ta sa gaba da kuma irin damar da masu saka jari daga Amurka suke dashi a kasar

Shugaba Buhari yace:

“Saboda kyakyawar dangantaka tsakanin kasashenmu Najeriya da Amurka sun sanya hannu akan wata yarjejeniya a shekarar 2010 da ta shafi tattalin arziki, diflomasiya, siyasa da tsaro. Yace saboda karfafa wannan yarjejeniya an gudanar da tattaunawa akan kasuwanci, makamashi, da aikin noma da gine-gine wadanda suka kara cudanya ta kasuwanci da saka jari tsakanin kasashen biyu. Yace ina son irin wannan cudanya ta cigaba ta kuma kara habaka domin inganta tattalin arziki da kasuwanci”.

Yace zan yi duk iyakan kokarina na samarda yanayi mai kyau da zai taimaka wurin saka jari a kasar a saukake da kuma cigaba da harkokin kasuwanci domin Najeriya it ace kasa da tafi kowace kasa girma a nahiyar Afirka. Yakamata Najeriya ta zama kasa ta farko da masu saka jari daga Amurka zasu yi tunanen zuwa domin mun fi kowace kasa yawan jama’a.

Buhari ya ambaci irin wuraren da Amurkawa zasu saka jari kamar makamashi da noma da iskar gas da hakan ma’adanai da yawon shakatawa da kuma sauran wuraren da ban a hakan man fetur ba saboda cin muradun shirin nan na AGOA.

Yayinda ya cigaba da jawabinsa Shugaba Buhari yace kodayake ya san hakin da ya rataya a kan gwamnati wurin samarda yanayi mai kyau ga harkokin kasuwanci da tattalin arziki dole ‘yankasuwa su taimaka da daukan nauyin habaka tattalin arziki da inganta kasuwanci a matsayin kokarin cigaba. Yace:

“Ya zama mana wajibi a Najeriya gwamnati da ‘yan kasuwa su tashi tsaye yayinda muke kokarin karkata harkokin tattalin arziki daga dogaro ga mai zuwa wasu fannonin. Musamman zamu yi maraba da wadanda suke son su zo Najeriya su saka jari a ayyukan hakan ma’adanai”.

Samarda aikin yi na cikin alkawuran kemfen da shugaban yayi. Yace zai yi iyakar kokarinsa ya cika alkawarin. Yace babu wata hanyar yin hakan illa habaka harkokin masana’antu da gine-gine da kafa kamfanoni. Shugaban ya sake jadadda kudurin Najeriya ta hada hannu da ‘yan kasuwa da zasu hada gwiwa da ita domin cimma muradunta na fadada tattalin arziki su kuma su kwashi tasu ribar.

Akwai abubuwa da yawa a Najeriya banda man fetur na kasuwanci saboda haka gwamnatinsa zata mayarda hankali akan bukatun ‘yan kasuwa. Yace zai kafa manufofin da zasu taimaka saboda samun cigaba. Gwamnatinsa zata rage barna da kudi da tabbatar da kowa ya amsa abun da yayi da yin mulki mai adalci. Dole kowa ya kiyaye da doka da kai’da kain da nain da bin yarjejeniya da kuma cire duk wani abu da ka kawo cikas wurin yin kasuwanci.

Yace:

Najeriya nada albarkatu da zasu habaka tattalin arzikinta amma bata da kudin da zata fitar dasu ba tare da taimakon kasashe kamar Amurka da ‘yan kasuwata ba. Saboda haka ku tuntubi masu tara jari kamar bankin fitar da shigar da kaya na Amurka su taimaki kasarmu.

Yace kamar yadda aka sani samun makamashi kodayaushe yana rage kudin yin kasuwanci. Saboda haka Najeriya na bukatar jari daga Amurka akan makamashi domin habaka wutar lantarki a Najeriya.

Yace ya san kalubalen da samarda wutar lantarki ke fuskanta a Najeriya kamar karancin iskar gas da fasa bututun mai da suka hana jama’a samun isasshiyar wutar lantarki.

Shugaba Buhari yace habaka tattalin arziki ba zai yiwu ba sai da ingantacen tsaro da kwanciyar hankali ba sai yace

“Saboda haka na maida hankali akan yakar Boko Haram tare da kasashe dake makwaftaka damu. Najeriya zata bada dalar Amurka dari ga rundunar yaki ta kasashen dake da hedkwata a kasar Chadi domin samar masu ingantattun kayan aiki da zasu murkushe Boko Hara. Ko watan jiya sai da Najeriya ta fara bada dalar Amurka miliyan 21. Da zara rundunar ta kafu ta kuma soma yaki da kungiyar Boko Haram Najeriya zata biya sauran kudin da tayi alkawarin bayarwa”

Daga nan shugaban ya godewa Amurka wadda ta bayarda taimakon dala miliyan biyar saboda yakar Boko Haram kana yace Najeriya zata kare kasarta ta kuma tabbatar wadanda aka rabasu da muhallansu sun koma su cigaba da rayuwa kamar yadda suka saba.

A karshe shugaban yace kasar tana cigaba da sayarda hannun jari a harkokin sadarwa da makamashi da iskar gas da ma’adanai da sufurin jiragen sama. Saboda haka ya gayyaci ‘yan kasuwa daga Amurka su yi anfani da wannan damar