Gwamnatin Ivory Coast Tana Shirin Kwace Makamai Daga Hanun Mayakan Sakai

'Yan gudun hijira daga Ivory Coast suke tafiya a gabashin Laberiya.

Wani babban jami’in ma’aikatar tsaron kasar Ivory Coast yace Gwamnati na shirin kwace dukkan makaman dake hannun mayakan sa kai sama da dubu goma

Wani babban jami’in ma’aikatar tsaron kasar Ivory Coast yace Gwamnati na shirin kwace dukkan makaman dake hannun mayakan sa kai sama da dubu goma a wani yunkuri na kawo karshen rikici da juna dake addabar kasar, da kuma tabbatar da ganin an maido da cikakken tsaro a Ivory Coast.

Kafofin labarun Ivory Coast jiya laraba, sun jiwo daga bakin mukaddashin Ministan tsaro Paul Koffi, yana cewa za’a kammala kwace makaman dake hannun mayakan sa kai nan ya zuwa karshen wannan shekarar da ake cki.

Ministan yace mayakan sa kan da aka kwace makamai daga hannunsu za’a janyo hankulansu da kwadaita masu shiga aikin sojin Gwamnati.