Accessibility links

Amurka tana matsawa Sudan lamba da neman a bincika batun aikata laifukan yaki


Wani sojan rundunar wanzar da zaman lafiya ta kasa da kasa yana sintiri a yankin Abyei (File)

Amurka tana matsawa kasar Sudan lamba ta bari masu bincike da basu da alaka da gwamnati su gudanar da bincike a jihar Kordofan bayanda Majalisar Dinkin Duniya ta bada rahoto cewa, an aikata laifukan yaki a wurin.

Amurka tana matsawa kasar Sudan lamba ta bari masu bincike da basu da alaka da gwamnati su gudanar da bincike a jihar Kordofan bayanda Majalisar Dinkin Duniya ta bada rahoto cewa, an aikata laifukan yaki a wurin.

Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Susan Rice, ta bayyana jiya Talata cewa, lamarin yana kara muni a kudancin Kordofan, inda dakarun dake goyon bayan arewa da kuma kudancin Sudan a wancan lokacin, suka yi fito mu gama a watan Yuni.

Tace Amurka ta damu ainun da rahotannin kisa ba gaira ba dalili da kaiwa farin kaya hari, da binne mutane da dama a manyan kabarbaru da kuma keta dokokin kare hakin bil’adama. Rice tace gwamnatin shugaba Barack Obama tana goyon bayan kiran da Majalisar Dinkin Duniya tayi na gudanar da binciken da ba na gwamnati ba a Kordafan dake kudanci.

Rahoton da cibiyar kare hakin bil’adama ta Human Rights ta bada jiya Litinin yana nuni da cewa, dakarun arewacin Sudan sun bude wuta a wuraren zaman farin kaya, a garin Kadugli, suka kashe mazauna wurin dake goyon bayan kudancin Sudan, suka wawashe gidajensu.

An yi gumurzun ne gabanin samun ‘yancin Sudan ta Kudu daga arewa a watan Yuli, bayan an shafe shekaru 6 ana yakin basasa. Gwamnatin Khartoum ta umarci tsofaffin mayakan kudancin Sudan su ajiye makamai ko kuma su kaura zuwa Kudu.

XS
SM
MD
LG