Gwamnatin Jihar Neja Ta Tsige Wasu Kwamishinoninta

Gwamnan jihar Neja a Najeriya, Alhaji Abubakar Sani Bello, ya kori yawancin kwamishinonin jihar daga kan mukamansu saboda rashin gamsuwa da kamun ludayin yadda suke gudanar da ayyukan cigaban al’ummar jihar.

Kwamishinoni uku daga cikin goma shatakwas da aka nada watannin baya ne kadai suka rage akan mukaman su yanzu. Wasu na ganin matakin na da nasaba da matsin lamba daga wasu ‘yan siyasa.

Alhaji Jibrin Baba Ndachi, kakakin gwamnan jihar Neja ya ce ba siyasa ce ta sanya gwamnan ya dauki wannan matakin ba, kundin tsarin mulkin Najeriya ya ba gwamnan damar yin haka idan da bukata.

Sai dai shugaban jam’iyyar adawa ta APGA a Neja Alhaji Aliyu Musa Liman yace daukar wannan matakin kusan ya zo a makare, kamata yayi ace an dauke shi tun lokacin da gwamnan ya nuna rashin gamsuwarsa da wasu daga cikin ‘yan majalissar sa.

Alhaji Kabiru Abbas, tsohon kwamishinan harkokin gona na daya daga cikin wadanda aka kora, ya ce komai da lokacin sa, haka Allah Ya tsara.

Masu sa ido akan harkokin mulki na ganin akwai bukatar gwamnan ya kara yin tankade da rairaya bayan korar kwamishinonin idan har an so talakawa su ci moriyar dimokradiyya.

Your browser doesn’t support HTML5

Gwamnatin Jihar Neja Ta Tsige Wasu Kwamishinonin Jihar - 3'33"