Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Bukaci Iyaye da Hukumomi Su Mutunta ‘Yancin ‘Ya’ya Mata Su Basu Ilmi


Ranar bikin yara mata
Ranar bikin yara mata

Ya kamata iyaye da hukumomi da sauran masu ruwa da tsaki su mutunta ‘yancin ‘ya’ya mata wajen basu ingantacen ilimin zamani da zai kyautata rayuwarsu, a cewar Kungiyar ‘Yan Mata

Kungiyar ‘Yan Mata da ake kira da turanci “Girls Brigade” ta jihar Filato, ta gudanar da bikin “Ranar ‘Ya’ya Mata” da Majalisar Dinkin Duniya ta kebe inda ta jaddadawa iyaye da mahukunta cewa baiwa ‘ya’ya mata ilmi shi ne ginshikin samar da ‘yan kasa nagari.

Shugabar makarantar Sakandaren Gwaji ta ‘yan mata dake garin Mista Ali a jihar Filato, Malama Mairo Jakada, tace yara mata suna fuskantar matsaloli da dama da suka hada da auren dole, rashin ilmi da matsanancin talauci. Tace sau tari iyaye maza sun gwammace su sa ‘ya’ya maza makaranta yayinda suke tura matan auren dole.

Alkalumma dai sun nuna cewa yara mata sama da miliyan 75 a fadin duniya ke fama da rashin ilmin zamani, yayinda daukan ciki ke hallaka yara mata ‘yan shekaru tsakanin 15 zuwa 19 a kasashe masu raunin tattalin arziki

Kwamishaniyar kungiyar “Girls Brigade” ta jihar, Madam Choji, tace manufar ranar ita don a dada fadakar da al’umma gameda martabar ‘yan mata ne.

Ga rahoton Zainab Babaji da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:02 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG