Gwamnatin Jihar Osun ta Kafa Dokar Ta-baci a Ile-Ife

Sarkin Ile Ife Ogunwusi

Biyo bayan rikicin da ya barke tsakanin Hausawa da Yarbawan Ile-Ife wanda ya yi sanadiyar hasarar rayuka da dukiyoyi, gwamnatin jihar Osun ta kafa dokar ta-baci domin dawo da zaman lafiya.

Dokar ta-bacin da gwamnatin jihar ta kafa ta kwanaki biyu ce kuma ta fara aiki ne daga karfe shida na yamma zuwa karfe bakwai na safe.

Mai baiwa gwamnan Osun shawara na musamman akan harkokin tsaro, Mr. Tope Adejumo ne ya ba da sanarwar kafa dokar saboda a sami zaman lafiya.

Ya ce wajibi ne a zauna lafiya da juna a kowane lokaci domin an dade tare.

Shi ma sarkin Ile Ife, Oba Ogunwusi, ya bukaci al'ummomin biyu dake rikicin da su zauna lafiya da juna, kana ya kira jami'an tsaro da su zakulo masu haddasa rikicin su kuma tabbatar an hukunta su.

Mataimakin kwamishanan 'yan sandan jihar Aminu Koji wanda ya ziyarci garin ya ce suna kokarin su ga cewa kowa ya zauna lafiya.

Ga rahoton Hassan Umaru Tambuwal da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Gwamnatin Jihar Osun ta Kafa Dokar Ta- baci a Ile-Ife - 1' 50"