Gwamnatin Najeriya na Shirin Samarma Matasa Aiki

Wasu matasa a taron shimfida zaman lafiya

Gwamnatin Najeriya na shirin samarma matasa aikin yi ta hanyar noman zamani da kiwon dabbobi da kifi cikin shekaru uku masu zuwa.
Gwamnatin Najeriya ta ce tana daukar matakan wani shiri na koyas da matasa kan noman zamani da kiwon dabbobi da kifi cikin shekaru uku masu zuwa.

Ministan aikin gona na kasar Dr. Akinwumi Adesina shi ya furta haka a wurin bude horon mako shida ga matasa a birnin Ibadan na jihar Oyo. Dr Adeshina wanda ya samu wakiltar Uwargida Oye Adeloye ya ce makasudin horon shi ne za'a tallafawa matasan su samu su tsaya da kansu. Za'a horar dasu a duk fannonin aikin gona domin su bunkasa abinci da aikin yi da hana zaman kashe wando a Najeriya. Ya kara da cewa za'a bada irin wannan horon a duk shiyoyi shida na Najeriya. Daya daga cikin masu bada horon Mr. Abdulkarim Abubakar ya ce matasa dari biyu ne zasu anfana da wannan kana za'a raba masu awaki dari da tumaki dari a karshen bada horon.

Hassan Umaru Tambuwal nada karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Gwamnatin Najeriya na Shirin Samarma Matasa Aiki - 2:00