Accessibility links

Tsohon Shugaba Hissen Habre Na Cadi Zai Gurfaba Gaban Kuliya Talatan Nan

  • Aliyu Imam

Tsohon shugaban kasar Cadi Hissen Habre

Shaidar da aka tara zuwa yanzu kan tsohon shugaban mulkin kama kariya na Cadi Hissene Habre, sun isa a tuhume shi da laifuffukan yaki,inji masu gabatar da kara.

Masu gabatar da kara a Senegal suka ce kwariya-kariyar shaidar da aka tara zuwa yanzu kan tsohon shugaban mulkin kama kariya na Cadi Hissene Habre, sun isa a tuhume shi da laifuffukan yaki, da cin zarafin Bil-adama, da gallazawa.

A talatan nan ne tsohon shugaba Habre zai bayyana gaban wata kotu ta musamman da aka kafa domin ta binciki zargin da ake yi masa na aikata laifuffuka zamanin da yake mulki tsakanin 1982 zuwa 1990.

Bayan shugabancinsa, Habre ya zauna cikin walwala a Senegal na tsawon shekaru 22 kamin ranar lahadi data shige ne hukumomi kasar suka bada umurnin a kama shi.
Yau talatan nan ne alkalan zasu tsaida shawarar ko su gabatar da tuhuma a hukumance kan tsohon shugaban kasar, ko kuma su kara wa’adin daurin talala da suka aza masa.

Babban mai gabatar da kara Mbacke Fall, yace shugaba Habre da kansa ya sa ido kan tsarin danniya a tsawon shekara takwas da yayi yana mulki a Cadi, yayinda yayi amfani da rundunar ‘yansanda kasar a matsayin makami na muzgunawa mutane.

Amma lauyan tsohon shugaban kasar Cadi El-Hadji Diouf, yace bai yarda da zargin da masu gabatar da kara suka yi ba, yana mai cewa: “duka kariya ce”. Yace babu yadda za a yi shugaban kasa ya san abunda yake faruwa a rundunar ‘Yansandan kasa ba.

Ana zargin tsohon shugaba Habre da sa ido wajen kashe abokan hamayyarsa su fiye da dubu 40,000, ta wajen cin zarafinsu sannu a hankali, da kuma keta haddin Bil-Adama.
XS
SM
MD
LG