Gwamnatin Najeriya Ta Umurci Hukumomi Su Inganta Rayuwar Matasa

Matasan Filato

Gwamnatin tarayya ta umurci dukkan hukumomi dasu maida hankali wajen gina fasahar matasa don samadda ci gaba a Najeriya.

Ministan matasa da inganta wasanni, Mr. Sunday Dare ya bayyana hakan yayin yaye wassu matasa 500 daga kananan hukumomi 5 na tsakiyar jihar Filato, da suka sami horo na musamman kan wanzadda zaman lafiya a yankunansu.

Gwamnatin Tarayya Ta Umurci Hukumomi Dasu Inganta Rayuwar Matasa

Ministan yayi jawabi akan zaman lafiyan da a shekarun baya Jihar Filato kedashi, ya bayanna muhimmancin horar da matasa sana'o'i da zasu dogara da shi, zai taimaka wajen kauda su daga shiga halayan banza kamar shan miyagun kwayoyi, kashe-kashe, sace mutane don neman kudin fansa, yin fyade, da dai sauran su.

Matasa A Jihar Filato

Ministan ya kuma kara cewa gwamnati ta umurci dukkan hukumoni da su dukkufa wajen inganta rayuwar matasa , da gina al'umma domin ci gaban kasa baki daya.

Saurari rahoto cikin sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

Gwamnatin Najeriya Ta Umurci Hukumomi Su Inganta Rayuwar Matasa