Gwamnatin Nijar Zata Ba Mata Gurabe A Zabe

Majalisar ministocn gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta kudiri aniyar karrama mata ta wajen basu guraben a zabe. Hakan ya biyo bayan kokawar da ko yaushe mata ke yi na maida su cikin cudanyar mulki, da rike mukamai. Musamman kasancewa suna ganin sune kan gaba a harkokin siyasa.

Matan sun koka ta yadda ake amfani dasu a wajen siyasa, da yakin neman zabe da sauran abubuwan da suka shafi siyasa, amma basu da gurbi mai yawa.

A kudirin gwamnati ta mika ma majalisar dokoki karin guraben mukamai na zabe daga kashi 15 zuwa 25, da kuma na nadin mukamai daga kashi 25 zuwa 30.

Saurari cikakken rahoton wakiliyar Muryar Amurka Tamar Abari.

Your browser doesn’t support HTML5

Gwamnatin Nijar Zata Karrama Mata A Guraben Mukamai A Zabe