Gwamnatin Tarayya taci alwashin shawo kan yaduwar zazzabin lassa

Maikatan asibiti suna jinyar wata mai fama da zazzabin Lassa

Gwamnatin Najeriya tace zata dauki matakin shawo kan bazuwar zazzabin Lassa a wadansu jihohin kasar ta wajen wayar da kan al’umma.

Gwamnatin Tarayya taci alwashin shawo kan yaduwar zazzabin lassa.

Gwamnatin tarayyar Najeriya tace, zata dauki matakin shawo kan bazuwar zazzabin Lassa a wadansu jihohin kasar ta wajen wayar da kan al’umma game da bukatar yiwa wadanda cutar ta kama jinyar gaggawa.Ganin irin asarar rayuka da ake yi sakamakon kamuwa da cutar.

Da yake jawabi ga manema labarai a birnin tarayya Abuja, karamin ministan lafiya, Dr Ali Pate yace daga watan Nuwamba shekara 2011 zuwa yanzu, an sami adadin mutane 397 da suka kamu da zazzabin lassa a jihohi goma sha daya inda daga ciki mutane 40 suka rasu.

Ya bayyana cewa jihohin da abin ya shafa sun hada da Edo, Nasarawa, Plateau, Ebonyi da kuma Taraba.

Sauran jihohin kuma sune, Yobe, Ondo, Rivers, Gombe, Anambra, Delta, and Lagos.

Zazzabin Lassa yana sa ciwon mara mai zafi da kuma atini da jini yayinda kimanin kashi 80% na wadanda suka kamu da cutar suke mutuwa.