Accessibility links

Najeriya zata shawo kan yaduwar cutar Polio kafin karshen shekara mai zuwa


Wani dan shekaru 57 wanda ciwon shann inna ya gurgunta

Darektan kiwon lafiya matakin farko na Najeriya yace, Najeriya zata magance yaduwar kwayar cutar shan inna kafin karshen shekara ta dubu biyu da goma sha uku

Darektan kiwon lafiya matakin farko na Najeriya Dr. Ado Gana Mohammed ya bayyana cewa, Najeriya zata magance yaduwar kwayar cutar shan inna kafin karshen shekara ta dubu biyu da goma sha uku.

Najeriya dai tayi kaurin suna sabili da kaza taka rawar gani a yaki da zazzabin cizon sauro. Lamarin ya kara muni ne sakamakon wani rahoto da Hukumar lafiya ta duniya (WHO) da shirin yaki da shan inna na duniya (Global Polio eradication Initiative GPEI) suka rubuta karshen watan Janairu cewa, za a ayyana kasar Indiya a matsayin kasar da ta shawo kan ciwon shan inna a cikin wannan wata na Fabrairu, bayanda aka shafe sama da shekara daya ba tare da an sami wani dauke da kwayar cutar ba.

Kafin wannan lokacin dai kasashen Pakistan, da Aghanistan da India da kuma Najeriya ne kasashe hudu rak a duniya da basu shawo kan cutar shan inna ba.

Hukumar lafiya ta duniya ta yabawa Najeriya a shekara ta dubu biyu da goma sabili da yakar cutar da kashi casa’in da biyar bisa dari. Sai dai a shekarar da ta gabata, an sami yaduwar cutar da kashi dari biyu da arba’in da hudu bisa dari.

Darektan kiwon lafiya matakin farko na Najeriya, ya bayyana cewa, “Har yanzu Najeriya tana cikin kasashe hudu rak dake fama da cutar shan inna a duniya duk da gagarumin ci gaban da aka samu a a shirin yaki da cutar. Cutar shan inna tana kara yaduwa inda aka sami yara hamsin da shida da cutar bara akasin ishirin da daya da aka samu a shekara ta dubu biyu da goma.”

Dr. Mohammed yace a halin yanzu ana samun masu dauke da cutar ne a jihohi takwas da suka hada da Kano, da Kebbi, da Jigawa, da Zamfara, da Katsina, da Sokoto, da Borno da kuma Yobe. Kashi 29% (mutane 16) na wadanda suke dauke da cutar suna Jihar Kano.

Darektan ya bayyana cewa, an sami koma baya ne bara sabili da kalubalar da aka fuskanta sakamakon kanfen neman zaben da aka gudanar a watan Afrilu inda hankali ya koma kan zabe, abinda ya sa aka yi watsi da shirin yaki da cutar. Sauran kalubalan kuma da aka fuskanta inji Dr. Mohammed sun hada da samun sababbin shugabannin siyasa. Bisa ga cewar darektan, duk da wadannan kalubalan, an yi kyakkyawan shirin shawo kan cutar.

XS
SM
MD
LG