Hanyoyin Najeriya, Sun Zama Makabartu Ba Mai Son Bi

Satar jama'a don neman kudin fansa a Arewacin Najeriya ya zama ruwan dare, da ake ganin babu wani abu da ya zama musiba ga al'umar a wannan lokacin kamar satar jama'a.

Wasu rahotannin na cewar cikin 'yan kwanaki biyu da suka gabata an sace mutane sama da 30 a hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Mutane na ganin cewar hakan nada nasaba da yadda mahukunta ke nuna halin ko in kula akan wannan lamarin, wata mata dake bayyana ra'ayinta da cewar, ai don ba'a gabatar da wani hukunci mai tsanani ne yasa matsalar ke kara ta'azzara.

A bangare daya kuwa Kaftin Garba Shehu mai ritaya, yana ganin cewar rashin samar da isassun kayan aiki, da jami'an tsaro a wadannan yankunan ke kara sa abun yana daukar wani salo.

Don haka akwai bukatar mahukunta su tashi tsaye wajen samar da matakai da suka dace, don kawo karshen wannan matsalar da ta saka jama'a cikin halin ha'ulail.

Hassan Maina Kaina ya hana muna wannan rahoton.

Your browser doesn’t support HTML5

Hanyoyin Najeriya, Sun Zama Makabartu Ba Mai Son Bi 2'10"