Hayakin Gawayi Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Matasa Biyu a Jos

Dakin Da Ya Kone Da Matasa a Garin Jos, Jihar Filato

Wasu matasa biyu sun gamu da ajalinsu bayan da suka hura wutar gawayi don dumama dakinsu saboda tsananin sanyin da ake fuskanta a wasu sassan Najeriya.

Tun dai a farkon wannan watan na Janairun 2020, sanyin hunturu mai tsanani ya sauka a cikin garin Jos da ke jihar Filato, da kuma wasu jihohin da ke Arewacin Najeriya,.

Hakan ya sa jama'a suka yi ta neman hanyoyin dumama jikinsu, da kuma makwancinsu.

Katifar dakin da matasan suka rasa rayukansu

Mamatan sun hada da Saminu Idris da abokinsa Idris Dahiru da ke unguwar Gangare a garin Jos da ke jihar Filato tsakiyar arewacin Najeriya.

Shaidu sun ce sun hura wutar gawayi ne suka rufe kansu a daki, inda hayakin gawayin ya suke su suka mutu.

Ko da yake, wani dan uwan daya daga cikin mamatan, ya ce ya ga kafar daya daga cikinsu ta kone a lokacin da ya balla dakinsu domin ya cece su.

Labiru Idris, wan Saminu Idris, wanda ya rasa ransa

A saurari cikakken rahoton Zainab Babaji cikin sauti daga jihar Filato:

Your browser doesn’t support HTML5

Hayakin Gawayi Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Matasa Biyu a Jos