Hotuna Kan Takaitattun Labaran Duniya Da Na Afirka a Yau

‘Yan sanda sun kama mutane biyar da ake zargin na da hanu a wani hari da aka kai akan wasu daliban Najeriya hudu a New Delhi, harin da ya kai ga kwantar da su a asibiti. Ranar Alhamis 30 Maris 2017

Wata bas din coci ta murkushe mutane 12 har lahira a karamar hukumar Uvalde dake Jihar Texas. Ranar Alhamis 30 Maris 2017. 

Firai Ministan Isra’ila Netanyahu na sa ran amince wa da gina sabbin gidaje a yamma da gabar Kogin Jordan nan da shekaru 20. Ranar Alhamis 30 Maris 2017.

Masu tsaron gabar tekun Italiya sun kai bakin haure 725 mafi yawancinsu ‘yan Afirka zuwa Sicily bayan da aka ceto su a tekun Meditareniya. Ranar Alhamis 30 Maris 2017.

Masu tsaron gabar tekun Italiya sun kai bakin haure 725 mafi yawancinsu ‘yan Afirka zuwa Sicily bayan da aka ceto su a tekun Meditareniya. Ranar Alhamis 30 Maris 2017.

Kungiyar ba da agajin kasa da kasa ta Red Cross ta fara sako kayan abinci daga jirgin sama a yankunan Sudan ta Kudu dake fama da matsananciyar yunwa. Ranar Alhamis 30 Maris 2017. 

Wata mota dauke da bam ta fashe a Bagadaza a jiya Laraba, inda ta halaka mutane 17 kana ta raunata wasu 60. Ranar Alhamis 30 Maris 2017

Shugaban Afirka ta Kudu Joseph Zuma ya sha alwashin korar ministan kudinsa da ake mutunta wa, matakin da ake ganin zai raba kan ‘yan jam’iyar ANC mai mulki. Ranar Alhamis 30 Maris 2017. 

‘Yan sanda sun kama mutane biyar da ake zargin na da hanu a wani hari da aka kai akan wasu daliban Najeriya hudu a New Delhi, harin da ya kai ga kwantar da su a asibiti. Ranar Alhamis 30 Maris 2017

Masana kimiyya a jami’ar Cambridge sun raini wani abu mai kama da bakwainin bera, wanda hakan shi ne ci gaba na farko a binciken da ake yi kan yadda halittu ke girma. Ranar Alhamis 30 Maris 2017.

Wata bas din coci ta murkushe mutane 12 har lahira a karamar hukumar Uvalde dake Jihar Texas. Ranar Alhamis 30 Maris 2017.