Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kai Mummunan Harin Ta'addanci a Babban Birnin Somaliyya


Babu wanda ya dauki alhakin harin da aka kai a birnin Mogadishu wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane bakwai.

Akalla mutane bakwai sun rasa rayukansu a yau Laraba bayan da wata mota dankare da ababen fashewa ta tarwatse a wajen wani gidan cin abinci a Mogadishu, babban birnin Somaliya.

Wurin cin abincin na kusa da ofisoshin ma’aikatun tsaron cikin gida da ta kula da harkokin matasa da wasanni.

Ya zuwa yanzu dai babu wanda ya dauki alhakin kai harin, amma ‘yan kungiyar al-Shabaab masu tsattsauran ra’ayi dake da alaka da al-Qaida sun sha kai makamantan wadannan hare-haren a baya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG