Hukumar Alhazan Najeriya Ta Bukaci Maniyyata Su Ba Da Kudin Ajiya

Hukumar alhazan Najeriya ta bukaci masu niyyar aikin hajjin shekarar 2020 da su ba da kudin ajiya kimanin Naira miliyan daya da rabi 1.5, a kashi uku ga hukumomin alhazansu na jihohi.

Hakazalika hukumar ta ba da har zuwa karshen watan nan na Oktoba ga kamfanonin jirgin yawo da su yi rijistar gudanar da aikin hajji mai zuwa don kauce wa rasa damarsu.

Wannan na kunshe ne a sanarwa daga jami’ar labarun hukumar Fatima Sanda Usara, wadda ta bayyana taro da masu ruwa da tsaki da komawa sabon ofishin dindindin na hukumar da a ka lakabawa suna “GIDAN HAJJI”.

Hukumar alhazan ta ce, shirin hajjin da ke tafe ya kunshi rejista kan lokaci, da biyan kudi kai tsaye na masauki ga masu gidaje don samun rangwame.

Shugaban hukumar alhazan Barista Abdullahi Mukhtar Muhammed, ya ce, cikin sabbin matakai akwai kaucewa cunkoson alhazan musamman a tantunan MUNA da hakan kan faru saboda rashin biyan kudi kan kari.

NAHCON ta ba da dama ga hukumomin alhazan jihohi su rika gudanar da lamuran UMRAH don fadada hanyar su ta kudin shiga, amma da sanya idon hukumar alhazan ta kasa don biyawa masu ibada hakkin su bisa irin kudin da su ka biya.

Ga cikakken rahoton Wakilin Muryar Amurka a Abuja, Nasiru Adamu El-hikaya.

Your browser doesn’t support HTML5

Hukumar Alhazan Najeriya Ta Bukaci Maniyyata Da Su Ba Da Kudin Ajiya