Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Bauchi Ta Kama Gungun 'Yan Fashi 72


A jihar Bauchi rundunar ‘yan sanda ta yi nasarar kama wasu rikakkun bata gari da suka addabi mazauna cikin garin Bauchi da kewaye, inda suke shiga gidajen mutane da daddare su na masu fashi da kuma sace-sace, har ila yau dai mutanen da aka Kaman ana zarginsu da satar mutane domin karbar kudaden fansa da kuma kisan kai.

Kafin nan mutanen sun aiwatar da ayyukan ta’addanci a unguwannin Tudun Salmanu, Water Board Quarters da kuma Unguwar Sarakuna.

Da yake gabatar da ‘yan fashin wa manema labarai jami’in hulda da jama’a na rundunar, DSP Kamal Datti, ya ce, wasu daga cikin barayin tuni an kaisu gaban alkali domin a yanke musu hukunci.

Har ila yau dai manema labarai sun ji ta bakin mutanen da ake tuhuma da yin sace-sace a unguwanni a cikin dare.

Ga cikakken rahoton wakilin Muryar Amurka a Bauchi, Abdulwahab Muhammad.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:58 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG