Hukumar IMF Ta Shawarci Najeriya Ta Kara Kudin VAT

Dan canji rike da dalar Amurka da kuma Naira

Hukumar bada lamuni ta Duniya IMF, ta shawarci gwamnatin Najeriya ta kara kudaden harajinta na VAT daga kashi bakwai da rabi cikin dari zuwa kashi goma cikin dari nan da shekara daya.

Hukumar ta kuma shawarta karin kashi 15 cikin dari nan da shekaru uku masu zuwa, saboda yanayi na mawuyaci halin da tattalin arzikin kasar ke ciki.

Hukumar IMF ta bada wannan shawarar ne a cikin wani rohoto da ta fitar da ta bayyana dalilanta na bada shawarar bisa ga la’akari da hawahawan farashin kayayyaki, da faduwar farashin mai, da kuma rashin ayyukan yi a kasar hade da matsalolin shugabanci, sai kuma annobar korona da ya kara dabaibaye lamura.

Shelkwatar IMF

Hukumar dai ta bukaci gwamnatin Najeriya da ta gaggauta sake fasalin tafiyar da tattalin arzikin kasar da

aiwatar da sauye sauyen da zasu bunkasa masu kanana da matsakaitan masana’antu, da kuma samar da ayyukan yi.

Daga cikin shawarwarin da Hukumar ta baiwa Najeriyar dai har da kara harajin VAT da ake dorawa kan kayayyakin da ake sayarwa wanda ake biyan kashi 7 da rabi yanzu, zuwa kashi 10 nan da shekara mai zuwa, da kuma kashi 15 nan da shekarar 2025.

hukumar-bada-lamuni-imf-tace-tattalin-arzikin-najeriya-ne-ya-fi-girma-a-afirka

basussukan-da-ke-kan-najeriya-sun-kai-naira-triliyan-31

riga-kafin-cutar-corona-zai-bunkasa-tattalin-arzikin-duniya---imf

Wannan shawarar ba ta samun karbuwa ga ‘yan Najieriya ba musamman yan kasuwa wadanda suka bayyana cewa daukar wannan matakin ba abinda zai haifar sai kara nawaita talakawa wadanda a halin yanzu suke cikin mawuyacin hali.

Ko a shekarar da ta gabata, gwamnatin Najeriya ta kara farashin kudaden harajinta na VAT daga kashi biyar cikin dari zuwa kashi bakwai da digo 5 cikin dari, lamarin da bai yiwa dubban “yan kasan dadi ba, kuma duk da korafi da kuma kushewa shirin, bai hana gwamnati kara kudin VAT din ba.

Saurari cikakken rahoton Shamsiyya Hamza Ibrahim cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

Hukumar IMF Ta Shawarci Najeriya Ta Kara Kudin VAT-4:00"


Karin bayani akan: IMF, VAT, Nigeria, da Najeriya.