Hukumar Yaki Da Cin Hanci A Nijar Ta Bayyana Samun Nasarori

HALCIA - Nijar

A Jamhuriyar Nijar hukumar yaki da cin hanci ta kasar, wato HALCIA ta bayyana samun nasarori a binciken da ta kaddamar game da wasu aiyukan da ake zargin an tafka a fannin hada-hadar man fetur, da kuma a cikin hukumomin biyan haraji, ko na fitan kaya.

Sai dai kungiyoyin fafitika sun nuna damuwa akan rashin hukunta wadanda aka kama da aikata laifin cin hanci a kasar.

A taron manema labaran da ya kira a wannan juma’a, ne shugaban hukumar yaki da cin hanci, mai shari’a Abdourahaman Ghousman, ya sanar cewa daga farkon wannan shekara ta 2019, har zuwa yau an samu korafe korafen sama da 180 wadanda aka sani suka ta'allaka akan yunkurin maghudi wajen biyan haraji, ko na awon kaya, ko choge a yayin bayar da kwangilar aiyukan gwamnati da dai sauransu…

Kasuwancin man fetur na daga cikin fannonin da hukumar yaki da cin hanci tace ta gano almandahana a game da yadda ake gudanar da su a Nijar, kamar yadda mataimakin hukumar ta HALCIA, Alhaji Salissou Oubandoma yayi karin bayani akai.

Tsarin samarda takardu da na awon motocin yan yawon shakatawa na daga cikin batutuwan da hukumar ta HALCIA ta gudanar da bincike akansu, inda a karshe ta bankado wani tsarin buga takardun jabu a wannan fannin.

Rashin hukunta masu laifika na daga cikin matsalolin dake tabaibaye aiyukan yaki da cin hanci a Nijar, saboda haka jami’in fafitika Abdou Elhadji Idi ke ganin akwai bukatar gyara..

Ga cikakken rahoton wakilin Muryar Amurka Souley Moumouni Barma.

Your browser doesn’t support HTML5

Hukumar Yaki Da Cin Hanci A Nijar Ta Bayyana Samun Nasarori