Hukumar Yaki Da Miyagun Kwayoyi a Najeriya Ta NDLEA Ta Lalata Tabar Wiwi

Hukumar NDLEA

Hukumar yaki da sha da safarar miyagun kwayoyi a Najeriya watau NDLEA a takaice ta lalata tabar wiwi da ta kama da ya kai ton goma sha hudu. Hukumar ta yi kira ga yan Najeriya da su taimakata mata a wannan yaki da take yi yan bata gari.

Shugaban hukumar na kasa Kanal Mustpha Abdallah da ya jagoranci lalata tabar wiwin, ya yi kira ga masu ruwa da tsaki a wannan yaki, da su hada hannu don yaki da miyagun kwayoyi. Kanal Mustapha yace yakamata har kasashen waje su bada gudunmawa ga yaki da miyagun kwayoyi.

Ganin barazana da miyagun kwayoyi ke yiwa lafiyar jama’a da tsaron kasa, wakilin gwamnan Abiola Ajimobi na jihar Oyo, wurin lalata miyagun kwayoyin, Cif Moses Adeyama yace duk wani filin da aka shuka tabar wiwi akai gwamnati zata kwace shi.

A ci gaba da maganarsa a madadin gwamnatin jahar Oyo, Cif Adeyama yace bayan kwace filin, hukuma zata kuma gurfanar da dasu gaban kotu.

A sakon gwamnan jahar Senata Ajimobi, ya bukaci jama’a musamman manoma su maida hankali wurin noman abinci da ake amfani dasu su daina noman tabar wiwi.

Your browser doesn’t support HTML5

NIGERIA DRUG