Hukumomin Australia Na Fargabar Ruruwar Sabuwar Wutar Daji

Wutar Daji A Australia

Hukumomi a Kudu maso Gabashin kasar Australia sun bukaci jama’a mazauna wasu yankuna kasar da su fice, yayin da ake fargabar wata gagarumar wutar daji za ta sake ruruwa sanadiyyar dawowar yanayin zafi mai tsanani da kuma kadawar iska mai karfi.

Wutar Daji A Australia

Al’ummar da ke yankin da ake kira Victoria, na daga cikin wadanda aka bukaci su fice daga yankin, kamar yadda Primiyan yankin Daniel Andrews ya fada.

“Za mu rika aikawa da sakonni ga jama’ar da ke yankin da wutar dajin ke ci, kuma sakonnin za su rika umartar mutane su fice daga yankin, domin ba mu da tabbacin za samu iya ba su kariya.” Inji Andrews.

Wutar Daji A Australia

Yanayin zafin ana tunanin zai haura sama da digiri 20 na ma’aunin Celsius a gobe Juma’a, wanda zai kawo karshen ruwan sama da yanayi mai sanyi da ya ba da wani dan lokaci na nunfasawa ga ma'aikatan kashe gobara

Wutar Daji A Australia

Wannan karin yanayi na zafi da aka samu, ya sa hukumomin jihar ta Victoria, suka kara tsawaita dokar ta-bacin da suka ayyana a makon da ya gabata zuwa tsawon kwanaki biyu.