Ibrahim Magu: Ba Za Mu Fasa Tsayin Daka Ba Wajen Yaki Da Barayi

Shugaban Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa Na Najeriya, Ibrahim Magu

Mukaddashin shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa na Najeriya Ibrahim Magu, ya ce ba zai fasa tsayin daka ba wajen yaki da barayin biro, da wadanda kan bullo da sabbin dabarun zarmiya.

Duk shugabannin hukumar ta yaki da cin hanci na nuna damuwoyi guda uku kan yakin, wadanda su ka hada da jinkirin shari’a a kotuna, da maida martani daga masu zarmiya, da kuma batagari da a ke samu a tsakanin jami’an.

Shugaban Hukumar Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa Na farko, Nuhu Ribadu

Shugaban hukumar na farko, Mallam Nuhu Ribadu, ya ce duk wanda ya samu matsayin jagoran yaki da cin hanci sai ya sadaukar da kansa, a kwai wahala domin yana yaki ne da masu karfi, da masu kudi, da kuma sauran jama'a.

Yaki da cin hancin ya fadada musamman ga masu damfara ta yanar gizo, da kuma hanyar hada-hadar kudi ta lataroni wato “BIT-COIN”.

Mustapha Mompha

Yanzu haka hukumar EFCC na cigaba da binciken wani fitaccen dan yanar gizo mai suna Mustapha Mompha wanda ke wasa da dalolin Amurka da sunan aikin canjin kudi a Dubai.

Ga rahoton cikin sauti daga wakilin Muryar Amurka, Sale Shehu Ashaka.

Your browser doesn’t support HTML5

Ibrahim Magu: Ba Zamu Fasa Tsayin Daka Ba Akan Yaki Da Barayi