Illar Coronavirus Ga Tattalin Arzikin Najeriya

Lagos

Najeriya ta sassauta dokar hana fita saboda coronavirus ne domin rage barnar da take yiwa tattalin arzikin kasar.

Matakin da aka dauka a ranar Litinin na zuwa ne bayan kwashe makwanni da rufe harkoki a fadin kasar wanda ya yiwa miliyoyin kasuwanci illa.

Najeriya ta sassauta dokar hana fita ta kwanaki 35 ne a Abuja da Legas da Ogun, bayan umarnin shugaba Muhammadu Buhari a makon da ya gabata a wani jawabi da ya yiwa kasar.

Shugaba Buhari ya yarda cewa hana mutane gudanar da ayyuka ya yi illa ga tattalin arzikin Najeriya, musamman a bangare kananan ayyuka da sai an yi su a kullum.

Sai dai shawarar sassauta dokar hana fitan na zuwa ne a lokacin da ake kara samun masu kamuwa da cutar coronavirus.

Alkaluman da cibiyar yaki da cututtuka masu yaduwa ta Najeriya NCDC ta fitar adadin ya ninka a makon da ya gabata, inda mutane sama da dubu biyu da dari biyar suka kamu ya zuwa ranar Litinin.