Iran Ta Sha Alwashin Mayar Da Martani Kan Kisan Janar Soleiman

Qasem Soleimani

Bayan da Amurka ta kai wani hari da ya yi sanadiyyar mutuwar kwamandan zaratan sojojin juyin juya hali na Qud, Oassem Soleimani, Iran ta sha alwashin mayar da martani.

Ministan Harkokin Wajen Iran, Mohammad Javad Zarif, ya kira kisan Janar din a matsayin keta 'yancin Iran da kuma aikata harin ta’addanci akan kasar.

Iraqi

Duk da dai cewar ma’akatar tsaro ta Amurka ta kare harin in da ta cewa, Janar din na da niyyar kai hare-hare kan jami’an diplomasiyya da ke Iran, shi dai shugaban Iran Hassan Rouhani ya ce, "tabbas, ba shakka, Iran da sauran kasashen duniya za su mayar da martani.”

Zanga Zanga a Iraq

Ita kuwa, Shugabar Majalisar Wakilan Amurka, Nancy Pelosi, ta yi Allah wadai da harin inda ta ce an kai shi ne ba tare da tuntubar majalisar ba.

Kuma a cewarta, wannan harin zai iya janyo karin rikice-rikice wadanda ba a bukata yanzu a duk fadin Duniya.