Jakadan Sudan Ta Kudu a Rasha Yayi Murabus

Shugaban kasar Sudan ta Kudu Salva Kiir

Jakadan Sudan ta Kudu a Rasha , Tela Ring Deng, yayi murabus a jiya Alhamis a cikin wata wasikar da ya aikewa shugaba Salva Kiir.

A wata hirar da yayi da shirin Muryar Amurka na “South Sudan In Focus” Deng ya tabbatar da murabus da yayi. Yace wasikar gakiya ce. "Na karanta kuma na sanya hannu akai."

An nada Deng Jakadan Sudan ta Kudu a Rasha a cikin shekarar 2014 bayan majalisar dokokin kasar ta ki amincewa da nada shi mukamin ministan shari’a.

Deng yaki bada dalilan da suka kai ga yanke wannan shawara na ajiye aikinsa a birnin Moscow. Yace yana so ya bada gudunmuwarsa ga zaman lafiyar Sudan ta Kudu a matsayin dan kasa mai zaman kansa.

Deng, shine babban jami’in diplomasiyar Sudan ta Kudu na biyu da yayi murabus, tun bayan da kasar ta samu yanci a shekarar 2011.. A cikin watan Yunin shekarar 2014, wani jami’in diplomasiyar Sudan ta Kudu Francis Nazario yayi murabus daga aikinsa na mukaddashin wakili a Majalisar Dinkin Duniya na dindindin, bisa dalilin gazawar gwamnatin shugaba Kiir ta sasanta rikicin kasar cikin ruwan sanyi.