Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane Miliyan Daya Da Rabi Za Su Fuskanci Fari a Sudan Ta Kudu


yara a Sudan ta Kudu

Tashin hankalin da Sudan ta Kudu ta jima tana fama da shi ya janyo mata matsalar karancin kudaden tafiyar da al’amurra inda har ma’aikatan ofisoshin jakadancin kasar a kasashe da dama suka jima babu albashi.

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa mutanen kasar Sudan ta Kudu kamar milyan daya da rabi na fuskantar barazanar mummunan fari, inda tace yanzu haka ma akwai mutane kamar dubu 20 da sun riga sun abka cikin matsanaciyar yunwa.

Mataimakiyar shugaban kwamitin bada jinkai ta MDD, Ursula Mueller, ta ce yanzu haka akwai mutane miliyan 5 - kusan rabin mutanen kasar ke nan, da ke fama da karancin abinci. Mueller tace kasawar mutane suyi noma saboda tashin hankalin da kasar ke fama da shi da kuma rashin muhallinsu ne suka janyo wannan matsalar.

Yayin da wannan ke faruwa ne kuma ake bada rahoton cewa kasar Sudan ta Kudu din ta rufe ofishin jakadancinta da ke Landan saboda ta kasa iya biyan kudin hayar ginin tun a watan Agustan shekarar da ta gabata.

Sai dai kuma wani kakakin Ma’aikatar Harakokin Wajen kasar, Mawien Makol ya gayawa gidan rediyon nan na Muryar Amurka cewa har yanzu basu sami wata takardar tada su daga ginin daga masu gidan ba, amma dai ya tabattar da cewa lalle ofishin na fuskantar karancin kudaden gudanar da ayyukansa.

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG