Jamhuriyar Niger Na Shirin Tura Sojojin Ta Mali

Rundunar Soji Niger

Kimanin sojoji 850, ciki har da mata 12 ne a ka yaye a lokacin bukin da aka shirya a garin Ouallam dake yankin Tilabery bayan da suka kwashe watanni 2 da rabi suna daukar horo akan dubarun yaki da ta’addanci.

Jakadan Amurka a Nijer, Eric P Whitaker ya ce wannan runduna na da nauyin tabbatar da tsaro a Mali musamman a yayin zaben ‘yan majalisar dokokin da kasar ke shirin gudanarwa a nan gaba, sannan za ta maida hankali wajen yaki da kungiyoyin ta’addancin da suka addabi arewacin kasar ta Mali.

Ministan tsaron kasar Nijer, Alhaji Kalla Moutari, ya gargadi wadannan dakarun dake shirin wakiltar wannan kasa a rundunar tsaron Majalisar Dinkin Duniya da ake kira MINUSMA a Mali.

"Kun sami dukkan wani shiri da zai baku damar gudanar da aiki a rundunar MINUSMA, inji Kalla Moutari. Ya kara da cewa da zarar kuka isa fagen fama kada ku manta cewa ku jakadun mu ne a Mali saboda haka ya zama wajibi a gareku ku gwada kwarewa da kishin zucci, da ladabi da biyayya, a takaice ku kasance abin koyi a kullum, koda yake ba shakka za ku bi sahun dakarun Nijer da suka gabace ku a wannan runduna ta MINUSMA.

Wannan ita ce runduna ta 7 da jamhuriyar Nijer zata tura zuwa Mali tun bayan da kasar ta rattaba hannu akan yarjejeniyar kafa rundunar hadin guiwar MINUSMA a karkashin inuwar Majalisar Dinkin Duniya a shekarar 2013.

Ga karin bayani a cikin sauti daga Souley Moumouni Barma.

Your browser doesn’t support HTML5

Jamhuriyar Niger Na Shirin Tura Sojojin Ta Mali - 2'35"