Jami’an Lafiya A Amurka Na Ta Gwada Lafiyar Fasinjojin Da Su Ka Fito Daga Kasar China

Jami’an Lafiya na Amurka sun bazu a filayen jirgin sama a San Francisco, Los Angeles da kuma New York, su na ta gwaje-gwayen lafiyar fasinjojin da su ka fito daga Wuhan, wani birni a yankin tsakiyar China, inda aka samu barkewar wata cutar mura mai shake numfashi.

Iyalai kan jira ne a farfajiyar matafiyan da su ka iso, yayin da ake ma fasinjojin da su ka fito daga Wuhan na kasar China binciken ganin ko shin su na dauke da cutar, wadda ta firgita jami’an lafiya a fadin duniya.

Johnny Tang, wani ma’aikacin fasahar komfuta a Silicon Valley na nan Amurka, wanda ke jiran iyayensa da za su kawo masa ziyara, ya ce: “Dayake sun san dama ziyarar da za su kawo shiryayyiya ce kawai, sun jinkirta na tsawon mako guda, su ka zauna a gida don kauce ma kamuwa da cutar.”