Jam’iyar PDP Ta Shiga Sabon Rudani

PDP

Jam’iyar PDP tana nazarin hanyoyin ceto shugabanta Uche Secondus daga rasa mukaminsa. Biyo bayan shigar da kara da tsohon mai ba Goodluck Jonathan shawarwari kan harkokin siyasa AhmedGulak ya yi yana kalubalantar zaben.

Gulok dai yana ikirarin cewa, zaman Secondus a matsayin shugaban jam’iyar ya sabawa doka. Uche Secondus dai ya zama shugaban jam’iyar na riko ne tun bayan yin murabus din Ahmed Mu’azu daga shugabanin jam’iyar bayan faduwarta zabe.

Ahmed Gulak yace, ya kamata Secondus ya sauka ya ba yankin arewa maso gabas dama ta zabi wanda take so ya kamala wa’adin mulkin Ahmed Mu’azu. Yace an zabi Secondus ne a matsayin mataimakin shugaban jam’iyar saboda haka bai kamata a ci gaba da kyaleshi ya rike mukamai biyu ba.

Gulak yace, idan ana so jam’iyar ta gyara kura kuran da suka dabaibayeta, kamata ya yi a dauki dukan matakan gyara.

Sai dai da yake maida martani, mataimakin sakataren watsa labarai na jam’iyar PDP, Abdullahi Jalo yace, masu wannan korafin sunyi garazaje, domin jam’iya tana sane da wannan batun, sai dai ana bukatar a samar da yanayin da ya dace kafin zaben cike gurbin.

Ga cikakken rahoton da wakilin Sashen Hausa Nasiru Adamu el-Hikaya ya aiko daga Abuja

Your browser doesn’t support HTML5

Siyasar jam'iyar PDP-2'44