Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

PDP Tayi Taron Yunkurin Farfado Da Jam'iyyar


PDP

Sakataren labarun jam’iyyar PDP, OLisa Metu, ya ce zasu yi yunkurin hade hancin ‘yan jam’iyyar

Babban taron yunkurin farfado da PDP, wanda shine irinsa na farko tun rasa madafin iko a karshen watan mayu bi samu hallatar akasarin iyayen jam’iyyar ba irinnsu Janar Babangida , Malam Adamu Ciroma, Adamu Maina Waziri, Ken Nnamani da sauransu.

Dama sakataren labarun jam’iyyar PDP, OLisa Metu, ya ce zasu yi yunkurin hade hancin ‘yan jam’iyyar ne na gaskiya don magance dalilan yasa suka fadi zabe.

A karo na farko PDP, ta bakin shugaban kwamitin taron Raymond Dopkesi, ta baiwa ‘yan Najeriya, hakunrin aikata ayyukan daya sanya ‘ya’yanta suka zama ‘yayan kuka masu jawowa uwarsu jifa.

Sanata Walid Jibrin, sakataren amintattun jam’iyyar ya ce abunda yakamata suyi shine na farko su yarda da ikon Allah.

A uzurin da ya bayar na rashin halartar taron Janar Babangida, ya ce ya zama dattijon siyasa da ya dace ya koma bayan fagge kuma da kaucewa take taken neman bashi takarar shugaban kasa a inuwa PDP,a shekara ta 2019.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG