Jihar Borno Na Nuna Damuwa Akan Hare Haren 'Yan Boko Haram Kwanan nan

Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya nuna damuwarsa game da hare haren da 'yan kungiyar boko haram ke kaiwa akan kananan hukumomi cikin 'yan kwana kin nan. Gwamnan ya dai bayyana wannan damuwar ne a lokacin da wani hadadden kwamitin majalisar dattawa da ta wakilai akan harkokin soja a karkashin jagorancin Sanata Mohammed Ali Ndume suka ziyarce jihar.

Ya ce jami'an sojan kasar na kokari, sai dai akwai bukatar a kara kaimi don tabbatar da cewa an kawo karshen irin hare haren da 'yan kungiyar boko haram ke kaiwa kan jama'a.

Gwamnan ya ce ko a jiya Asabar sun sami kwararan bayanai dake nuna cewa 'yan kungiyar boko haram sun yi yinkurin kai wani hari a garin Gubio wanda jami'an soja suka dakile, amma abbin tambaya a nan shine har tsawon wani lokachi zamu ci gaba da kasancewa cikin wannan lamari? Dole ne mu samar da mafita akan wannan lamari.

Ya kuma yaba da kokarin da sojan ke yi duk da cewa a yanzu haka ana fuskantar hare hare a wasu kananan hukumomi guda uku cikin makwonni uku, amma jami'an soja sun barar da dukan wadannan hare-haren da hadin gwiwar civilian JTF, da kuma maharba. Muna yaba masu kuma muna yabawa gwamnatin shugaba Muhmmadu Buhari game da yada ya maida hankali akan jihar.

Sanata Mohammed Ali Ndume dai shine shugaban kwamitin sojan na majalisar Dattawa da kuma ya jagorance kwamitin.

Ga karin bayani cikin sauti daga Haruna Dauda.

Your browser doesn’t support HTML5

Jihar Borno Na Nuna Damuwa Akan Hare Haren 'Yan Boko Haram Kwanan nan