Jihar Jigawa, ta Dauki Matakan Tantance Jama’ar Dake Shiga Jihar

Yankin Maigatari, na jiran kayyakin aiki dangane da kariyan Ebola.

Hukumar kiwon lafiya na kan iyaka ta jihar Jigawa, ta dauki matakan tantance jama’ar dake shiga jihar, masaamman ta Maigatari, saboda kasuwar dabbobin dake garin.

Jami’in kiwon lafiya, na hukumar dake, jihar ta Jigawa, Kabir Ibrahim, ne ya furta haka a wata hiran da sukayi da wakilin mu Muhamud Ibrahim Kwari.

Ya kara da cewa har yanzu yankin na Maigatari, na jiran kayayyakin aiki na dangane da kariyan Ebola kamar yanda aka yi alkawarin kawowa.

Shi kuwa kwamishinar lafiya, na jihar Jigawa, Dr. Tafida Abubakar, kuma shugaban kwamitin da gwamnatin jihar Jigawa , ta kafa domin yaki da cutar Ebola, yace dangane da wannan wunkurin yasa suka shigar da kugiyoyin masu motocin sifiri cikin kwamitin yaki da wannan cutar.

Sakataren, Kungiyar, direbobin sifiri reshen maigatari Kabir Ibrahim,yace har yanzu fadakarwa kan cutar Ebola, bata kai garesu ba, kamar yanda ya yiwa wakilin muryar Amurka bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Shirin Ebola - 3'35"