Jihar Neja Zata Amince da Aiwatar da Hukuncin Kisa

Gwamnan Jihar Neja Alhaji Abubakar Sani Bello

Gwamnan jihar Neja Alhaji Abubakar Sani Bello yace ashirye yake ya sanya hannu ga duk wani hukumcin kisa da wata kotun jihar ta yanke wa duk wanda aka samu da laifin kisan kai.

Gwamnan yana magana ne a wani babban taron masu ruwa da tsaki akan harkokin ilimi da aka gudanar a Minna.

Alhaji Abubakar Sani Bello ya nuna bacin ransa akan yadda wasu suke anfani da kabilanci ko addini domin tayarda fitina tsakanin al'umma.

Yace da yaddar Allah idan har an kama wani wanda aka samu da laifin kisan kai to "zan yi misali dashi". Yace idan kuma an yankewa wasu hukumcin kisa bisa gaskiya kuma babu tababa ko shakka a kawo masa takardar kisar zai sa hannu

Gwamnan ya nuna damuwa akan wani sabon rikici da yayi sanadiyar mutuwar mutane bakwai tare da kona gidaje da dama tsakanin kabilar gwarawa manoma da fulani makiyaya a kauyen Sabon Daga da ke yankin Bosso cikin makon da ya gabata.

Acewar gwamnan rasa doya ko dari ne bai kai ran mutum ba. Ana iya maida doya amma ba za'a iya maida rai ba. Ya kara da cewa jihar bata da matsalar banbancin addini ko na kabilanci amma akwai wasu daidaikun mutane dake labewa da addini da kabilanci suna haddasa rikici.

Gwamnan ya kara da cewa ba za'a iya kawo cigaba a jihar ba a cikin yanayin rashin tsaro.

Ga rahotn Mustapha Nasiru Batsari.

Your browser doesn’t support HTML5

Jihar Neja Zata Amince da Aiwatar da Hukuncin Kisa - 3' 00"