Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Taraba Ya Yi Murabus

Darius Dickson Isiyaku

Zaben sabon kakakin Majalisar Dokokin jihar Taraban bai zo da mamaki ba, sakamakon rashin jituwa da ke wakana a tsakanin tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Abel Peter Diah, da kuma gwamnan jihar Taraba Akitek Darius Dickson Isiyaku, wanda tun farko ake zargin ya fidda miliyoyin Naira domin wannan tabargazar.

Abel Diah Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Taraba Mai Murabus

Kuma ganin irin tarkon da zai iya fadawa, sakamakon sanya hannu a takardar tsigewa da wasu 'yan majalisa fiye da goma su ka yi, sai kakakin Majalisar Abel Diah ya bada takardar murabus.

A zaman 'yan majalisar na yau Litinin ne aka zabi sabon kakakin majalisar Joseph Alkinjo Kunini, kana kuma aka zabi Hamman-Adama Abdullahi a matsayin sabon mataimakin kakakin majalisar.

Majalisar Dokokin Jihar Taraba

A tambayar da aka yi ma sabon kakakin game da wannan sabon kujera da ya samu, yayi karin haske ne game da cece-kuce da dambarwa na majalisar dokokin jihar Taraban.

An dai zargi gwamnan jihar Taraban, Darius Dickson Isiyaku, da zama kanwa uwar gami wajen sauya kakakin majalisar. Zargin da shi gwamnan ke cewa ba haka lamarin yake ba.

Saurari rahoto cikin sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Taraba Ya Yi Murabus