Kalaman Buhari Sun Haifar Da Ce-Ce-Ku-Ce

Shugaba Buhari A Taron Shugabannin Jam’iyyar APC Inda Ya Bayyana Niyyarsa Na Sake Neman Wa'adin Shugabanci

Kalaman da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi na cewa duk wanda ya saci akwatin zabe “ya yi hakan ne a bakin ransa,” sun haifar da ka-ce-na-ce a fagen siyasar kasar.

Buhari ya bayyana hakan ne a wajen wani taro da jam’iyyarsa ta APC ta shirya a Abuja.

Tuni jam’iyyar adawa ta PDP ta bayyana furucin a matsayin salon mulkin “kama karya,” tana mai cewa hakan zai sa dakarun kasar su rika daukar doka a hannunsu.

“Komai za a yi a bi kundin tsarin mulkin kasa, abin da kundin tsarin mulki ya ce shi ne, idan an samu mutum yana laifi a kamo shi a tuhume shi.” Inji daya daga cikin jagororin da ke yi wa Atiku Abubakar kamfe, Malam Umar Sani.

Sai dai kakakin shugaban kasar, Malam Garba Shehu, ya ce an yi wa shugaban mummunar fahimta, “saboda halin da ake ciki na siyasa.”

“Hakika Shugaba Muhammadu Buhari gargadi yake yi ga ‘yan banga da masu zuwa suna kwatar akwatin kuri’a su gudu da su don su je su dangwala hannu a yi cuta.” Inji Garba Shehu.

Garba ya kara da cewa, ana yawan samun irin wannan matsala a yankin kudancin Najeriya, dalilin kenan da ya sa a ja kunne.

“Saboda haka, in an dauka ana ba shi wata ma’ana cewa ya yi a yi harbi, ai akwai doka.” Inji Garba Shehu.

A ranar Asabar mai zuwa, 'yan Najeriya za su kada kuri'unsu a zaben shugaban aksa da an 'yan majalisu.

A wasu lokuta, babban zabe a Najeriya kan zo da kalubalen masu satar akwatunan zabe.

Saurari cikakkiyar hirar da Umar Faruk Musa ya yi da Malam Garba Shehu da kuma Malam Umar Sani:

Your browser doesn’t support HTML5

Kalaman Buhari Sun Haifar Da Ce-Ce-Ku-Ce - 2'51"