KANO: Yau Majalisar Dokoki Za Ta Yi Wa Sabon Kudurin Dokar Kafa Masarautu Karatu Na Biyu

Gwamnan Jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje

Majalisar Dokokin Jihar Kano na kudurin yin karatu na biyu kan Daftarin Dokar Kafa Sababbin Masarautu hudu da kotu ta rushe a jihar.

Bayan da gwamnatin jihar Kano ta mika sabon kudurin dokar kirkiro sababbin masarautu hudu a jihar daga tsohuwar masarautar Kano ta yanzu, majalisar dokokin jihar ta fara nazari a kan kudurin, inda tuni ya sami karatun farko a zauren majalisar.

Matakin ya biyo bayan rushe sarautun hudu na Bichi, Karaye, Rano da Gaya da babbar kotun jihar Kano karkashin jagorancin Mai Shari’a Usman Abba ta yi, kimanin makwanni biyu da suka gabata.

Kwamishinan shari’a kuma na jihar Kano Barista Ibrahim Mukhtar ya ce kotun ba ta amince da dokar da majalisar dokokin jihar ta yi na kafa masarautun ba saboda kura-kuran da majalisar ta yi wajen samar da dokar, dalili ke nan da ya sa suka dauki sabon matakin bayan nazarin hukuncin kotun.

Bayan kammala nazartar hukuncin ne, gwamnatin Kano ta yanke shawarar shirya sabon kudirin kuma ta mika shi ga zauren majalisar domin amincewa.

A cikin wata wasika ga shugaban majalisar, gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya nanata muhimmancin kafa masarautun ga sha’anin tsaro, kiwon lafiya, ilimi da kuma zamantakewar al’uma.

Majalisar dai ta yi karatu na farko ga daftarin sabuwar dokar, kuma shugaban masu rinjaye a majalisar Hon Labaran Abdul Madari ya yi Karin haske kan lamarin tare da bayyana cewa, suna yi ne tare da neman ra’ayoyin jama’a.

Hakan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da masu kula da lamura ke ci gaba da tsokaci dangane da wannan batu.

Malam Kabiru Sa’idu Sufi ya ce “kamata yayi talakawa su dubi lamarin da idon basira, a bangaren shugabannin kuma, kamata yayi su yi la’akari da abin da al’ummar su ke bukata, ba wai bukatun kan su ba”.

Ga karin bayani daga Mahmud Ibrahim Kwari

Your browser doesn’t support HTML5

Sabon Kudurin Dokar Sababbin Masarautu a Jihar Kano