Kasuwannin Hannayen Jari Na Ci Gaba Da Faduwa A Duniya

A jiya Laraba Hukumar Lafiya ta Duniya – WHO, ta ayyana cutar Coronavirus a matsayin annoba, biyo bayan bullar cutar a kasashe 114.

A yayin da Amurka ta ba da sanarwar hana tafiye-tafiye zuwa turai, ita kuma hukumar kwallon Kwando ta NBA, ta ce ta dakatar da wasannin ta a halin yanzu.

Shugaban hukumar ta WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesu ya fada a jiya Laraba ECWA, "A cikin makwanni biyu da suka gabata, adadin wadanda suka kamu da cutar ta COVID-19 a wajen China, ya ninninka har sau 13, yayin da kuma yawan kasashen da lamarin ya shafa shi ma ya ninka sau uku” .

A halin da ake ciki kuma kasuwannin hannayen jari na ci gaba da faduwa a yau Alhamis, sakamakon ci gaba da yaduwar cutar ta coronavirus, da kuma shafar tattalin arziki da take yi.

Farashin hannun jarin NIKKEI na kasar Jamus ya fadi da kashi 4.4 bisa dari, yayin da na kamfanin Seng a Hong Kong ya fadi da kashi 3.7%. kasuwannin hannayen jarin Australia ma sun fadi warwas da kashi 7% a yau Alhamis.

Lamarin ya kuma shafi kasuwannin hannayen jarin nahiyar turai a farkon ranar yau, inda a Britania da Faransa da Jamus suka fadi da kashi 6%.