Kotu ta umarci gwamnatin soji a hamhuriyar Niger ta saki tsohon shugaban kasar

Tsohon shugaban kasar Jamhuriyar Niger Mamadou Tandja

Kotun kungiyar cinikayya da bunkasa tattalin arzikin kasashen Afirka ta yamma ECOWAS, a zaman da tayi a birnin tarayyar Nigeria Abuja yau litinin,ta yanke hukunci tare da baiwa shugabannin mulkin sojin kasar Niger umarnin sakin tsohon shugaban kasar Mamadou Tandja da aka hambaras a juyin mulki.

Kotun kungiyar cinikayya da bunkasa tattalin arzikin kasashen Afirka ta yamma ECOWAS, a zaman da tayi a birnin tarayyar Nigeria Abuja yau litinin, ta yanke hukunci tare da baiwa shugabannin mulkin sojin kasar Niger umarnin sakin tsohon shugaban kasar Mamadou Tandja da soja suka hambaras a juyin mulkin da suka aiwatar. A watan Fabarairu ne rundunar sojin jumhuriyar Nijer ta hambaras da Gwamnatin farar hula karkashin jagorancin Mr. Tandja, watanni shida bayan tilasta yin sauye-sauye a kundin tsarin mulkin jkasar domin bashi damar ci gaba da mulki. Shugabannin sojin da suka yi juyin mulkin sun yi alkawarin maida mulki ga farar hula bayan gudanar da zaben a watan Afrilu mai zuwa.