Kotu Ta Yanke Wa Orji Kalu Hukuncin Shekara 12

Tsohon Gwamnan Jihar Abia Orji Kalu

Wata babbar kotun tarayya da ke Legas a karkashin mai Shari'a Mohammed Idris ta yanke wa tsohon Gwamnan Jihar Abia Sanata Orji Uzor Kalu, hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekara 12.

Sanata Orji Kalu ya kasance gwamnan jihar Abia ne daga shekara 1999 zuwa 2007. Yanzu kuma mamba ne a jam'iyya mai mulki ta APC.

An gurfanar da Sanata Orji Kalu ne tare da kamfaninsa mai suna Slok Nig. Ltd tare da tsohon darakatan kula da asusun kudaden gidan gwamnatin jihar Udeh Udeogu, a lokacin da Orji Kalu yake Gwamnan jihar.

Kotu Ta Baiwa Tsohon Gwamna Orji Kalu Shekara 12 A Gidan Yari

A cikin tuhume-tuhume 39 da hukumar EFCC ke yi wa wadanda aka daure, an zarge su ne da hada baki wajen karkatar da Naira Biliyan 7.6 mallakar al'ummar jihar Abia da suka mayar dukiyarsu.

Lauyan gwamnati wanda ya gabatar da karar, ya ce tsohon gwamnan ya saba wa sashe na 17 a dokar haramta safarar kudi ta shekara 2004 wacce aka tanadar wa hukunci sashe na 16 na kundin dokar.

Tsohon mukaddashin shugaban kungiyar kwadago ta kasa Comrade Isa Tijjani, ya ce, wannan hukunci yana nuni da cewa an fara samun ci gaba a yaki da cin hanci da rashawa da gwamnatin Mohammadu Buhari ke ikrarin tana yi, kuma ya yaba da ganin haka.

A saurari rahoto cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

Kotu Ta Yanke Wa Orji Kalu Hukuncin Shekara 12