Kotun Kolin Jamhuriyar Niger Yayi Watsi da Kararda Mahaman Usman ya Shigar

Mr. Morou Amadou ministan shari'a na Jamhuriyar Niger

A Jamhuriyar Niger kotun kolin kasar yayi watsi da karar bangaren Mahaman Usman na jam'iyyar CDS ya shigar.
Wani kotun koli dake Niamey a Jamhuriyar Niger yayi watsi da kararda bangaren Mahaman Usaman na jam'iyyar CDS ya shigar yana kalubalantar bangaren Abdu Labbo.

Bangaren Mohaman Usman ya kai bangaren Abdu Labbo kara ne bisa ga korar da aka yiwa shi Mohaman Usman tsohon shugaban kasar da magoya bayansa. Jam'iyyar CDS Rahama ta kori 'yan jam'iyyar ne domin sun buturewa kudirin uwar jam'iyyar tare da marawa dan takarar jam'iyyar PNDS Tarayya yayin fitar da gwanin tsayawa takarar shugaban kasa da aka yi a shekarar 2011. Tun daga wannan lokacin takaddama ta kunno kai tsakanin 'yan jam'iyyar ta CDS tare da zuwa kotuna daban daban lamarin da ya kaisu har ga kotun kolin kasar.

Mainasara Umaru lauyan da ya kare bangaren Abdu Labbo yace kotun koli ta yanke shari'a tace bangaren Abdu Labbo ke da gaskiya. Amma kuma bangaren Mahaman Usman sai suka ce ai ita kotun kolin ta yi kuskure a shari'arta. Sun bada wasu hujjoji kotun tace su dawo za'a bincika. To a wannan hukucin kotun ta tsayar da magana. Babu wata magana kuma domin ta ba bangaren Abdu Labbo kaskiya.

Yanzu dai a bangaren Mahaman Usman alkalaminsu ya riga ya bushe. To sai dai bangaren Mahaman Usman na shirin kai karar kotun kolin a kotun CEDEAO ko ECOWAS dake Abuja babban birnin Najeriya.Lauyan Mahaman Usman yace hukuncin da aka yi bai dace ba. Domin haka zasu garzaya Abuja.

Your browser doesn’t support HTML5

Kotun Kolin Jamhuriyar Niger Yayi Watsi da Kararda Mahaman Usman ya Shigar - 3:16