Accessibility links

Jam’iyyun Dake Mulki A Jamhuriyar Nijar Sun Yi Gangami

  • Garba Suleiman

Mahamadou Issoufou, a hagu, da Seini Oumarou a dama suna gaisawa

Magoya bayan jam’iyyun dake mulki daga duk fadin Nijar sun hallara a Yamai a wani gangamin da aka bayyana a zaman tauna tsakuwa domin aya ta ji tsoro

Magoya bayan jam’iyyun da suke mulki a jamhuriyar Nijar daga duk fadin kasar sun amsa kiran da shugabanni suka yi musu, inda suka hallara a birnin Yamai domin gudanar da wani gangamin nuna cewa a shirye suke su takali gungun ‘yan adawar dake ci gaba da kalubalantar masu ikon kasar.

Shugaban jam’iyyar PNDS-Tarayya mai mulkin kasar, Bazzoum Mouhammad, yace jam’iyyun adawa sun a kokari ne su toshe duk wata kafar da ita PNDS da kawayenta zasu iya aiki ga jama’ar kasa, domin har a je ga lokacin zabe su rika cewa babu abinda aka tabuka a jamhuriya ta 7 karkashin jagorancin shugaba Issoufou Mahamadou.

Shugaban na jam’iyyar PNDS-Tarayya ya zayyana ayyukan da yace sun gudanar ga kasa, akasin rashin aikin komai na masu adawa da su wadanda a can baya suka shafe lokaci mai tsawo sun a mulkin Jamhuriyar Nijar ba tare da sun yi mata wani abin kirki ba.

Wani jami’in jam’iyyar Lumana Afirka mai adawa, Malam Salisu H.M. Salisu, wanda ya halarci wannan gangami na jam’iyyun dake mulkin, yace sun amsa kiran shugaba Issoufou Mahamadou ne na samun hadin kan kasa wajen gudanar da ayyuka, ya kuma nanata cewa sun je da sunan a hada kai a yi ma jama’a baki daya aiki.

Yace aikin gina kasa na kowa da kowa ne, ban a shugaban kasa shi kadai ba.

Shi ma Al-Badei Abouba na jam’iyyar MNSD wanda ke cikin gwamnati y ace zasu ci gaba da bayarda goyon baya ga shugaban kasar har sai lokain da yace bay a bukatar goyon bayansu.
XS
SM
MD
LG