Kungiyar Hizbah Za Ta Dauki Mataki Akan Matasa Masu Cin Abinci Da Rana A Watan Ramadan

Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje (Facebook/Gwamnatin Kano)

Yayin da Ibadar azumin watan Ramadana ta kankama a tsakanin musulmin duniya, hukumar Hizbah a jihar Kano a Najeriya, tayi karin haske dangane da gargadin da tayi.

KANO, NIGERIA - Hukumar ta Hizbah ta sha alwashin daukar tsauraran matakai akan matasa dake badalar cin abinci da rana a sassan jihar a cikin wannan wata na Ramadana. Sai dai Malamai sun ce tilas ne iyaye su kara kaimi wajen bada tarbiyyar da ta dace ga ‘yayan su kafin a cimma buri.

Hukumar Hizbar a jihar Kano wadda wata doka da majalisar dokokin jihar ta kafa a shekara ta 2004, kuma yanzu haka take da dakaru fiye da dubu tara, ita ce ke da alhakin aikace-aikacen umarni da kyawawan ayyuka da kuma hani daunana a tsakanin al’umar jihar.

A farkon makonnan ne, kwamadan hukumar ya fitar da wata sanarwa dake jan kunne da yin gargadi ga matasa masu bujurewa dokokin azumin Ramadana suna ciye-ciyen abinci da rana kuma a bayyanar Jama’a, yana mai cewa babu ko shakka jami’an hukumar zasu saka kafar wando guda da matasa masu irin wannan hali.

Ku Duba Wannan Ma An Kaddamar Tambarin Tashar Sauke Hajar Teku A Jihar Kano

Ana su bangaren, Malamai sun ce akwai bukatar iyaye su kara himma wajen cusa tarbiyyar da ta kamata ga ‘ya’yan su, musamman matasa, domin kubutar dasu daga halaka da ma sauran Jama’a.

Malam Mustafa Muhammad Dandume na cibiyar da’awa da Mu'azu bn Jabal a nan Kano ya yi bayani akan wadanda shari’ar musulinci ta halartawa sha ko cin abinci da rana cikin watan Ramadana, saboda da lalura.

Saurari rahoto cikin sauti daga Mahmud Ibrahim Kwari:

Your browser doesn’t support HTML5

Kungiyar Hizbah Za Ta Dauki Mataki Akan Matasa Masu Cin Abinci Da Rana A Watan Ramadana