Kungiyar ISIS Ta Dauki Alhakin Harin Da Aka Kai Majami'ar Kubdawa

Gawarwakin mutanen da suka mutu a harin Majami'ar Kubdawa

Kungiyar Da’esh, wacce aka fi sani da ISIS, ta dauki alhakin harin bam na kunar bakin waken da aka kai ranar Lahadi, a majami'ar Kubdawa da ke birnin alKhahira da ya yi sanadin mutuwar mutane akalla 25.

Faifan hotan bidiyo na talabijin ya nuna wanda ake zargi yayin da yake shiga kofar majami'ar kafin ya tarwatsa kansa.

Kungiyar Da’esh ta bayyana mutumin a matsayin “Abu Abdullah al-Masri” wanda ake zaton inkiya ce kawai. A ranar litinin Shugaban kasar ta Masar Abdel-Fattah el-Sissi, ya bayyana dan kunar bakin waken da suna Mahmoud Shafiq Mohammed Mustafa, dan shekaru 22 da haihuwa.

Jami’an tsaro na Masar sun tsare mutane hudu da ake zargin suna da hannu a harin, sannan suna neman wasu ragowar.

Yan kungiyar ta Da’esh sun yi gargadi akan wasu hare haren a wani bayani da suka bayar a rubuce ashafinsu na yanar gizo a ranar Talata, tare da alkawarin cigaba da yakar abin da su ka kira "duk wani Kafiri ko kuma wanda ya i ridda a Masar da kuma sauran wurare."