Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dinkin Duniya Ta Samu Sabon Babban Sakatare


Sabon Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, MDD, Antonio Gutarres

A jiya ne aka rantsarda Antonio Guterres na kasar Portugal a matsayin sabon babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, ko MDD a takaice

A jawabinsa na kama aiki, sabon sakataren yace MDD na bukatar ta rage “dogon turanci”, ta fi maida hankali wajen “cika aiki.

Shi dai Guterres, 67, wanda tsohon frayim-ministan Portugal ne kuma tsohon shugaban cibiyar kula da ‘yan gudun hijira na MDD, ya kada mutane 12 ne a gasar neman wannan mukamin.

Ganin irin matsalolin da duniya ke fuskanta, wadanda suka hada da kalubalen ‘yan gudun hijira, yake-yake a kasashen yankin Gabas ta Tsakiya da na Afrika, barazanar ta’addanci da maganar chanjin yanayi, ana ganin cewa sabon sakataren na da aiyukka da yawa da zasu dauke mishi hankali na wani lokaci mai tsawo bayan ya karbi aikin daga hannun sakatare mai barin gado, Ban Ki-moon a ran 1 ga watan Janairun sabuwar shekara.

Tsohon Sakatare Ban Ki-moon da sabon Antonio Gutarres
Tsohon Sakatare Ban Ki-moon da sabon Antonio Gutarres

XS
SM
MD
LG