Kungiyar Likitoci Ta Nijar Ta Fara Babban Taro Na Kasa

Aikin magani a Nijar

Kungiyar kwararun malaman assibitoci da ake kira SYMFAMED ta fara wani babban taro a garin Maradi da gurin ganin likitoci sun bada gudummuwa ga yunkurin cimma muradun karni da Majalisar Dinkin duniya ta sanyawa gaba,

Kungiyar likitocin tace taron zai bata damar nazarin matsalolin dake hana ruwa gudu a fannin aikin kiwon lafiya su kuma nemi hanyoyin warwaresu da nufin ganin an fitar da Nijar daga jerin kasashen da suke baya baya. Kungiyoyin tace zata kuma ba gwamnati shawarwari da ta kyautata zaton idan aka yi amfani da su za a sami ci gaba.

Kungiyar likitocin ta koka dangane da rashin kayan aiki issasu a cikin assibitocin kasar da kuma karancin likitoci. Suka kuma yi kira ga hukumomi su tura Karin mutane karatu a wannan fannin domin samun likitoci da zasu koma suyi ‘yan Nijar aiki.

Taron da ya sami halartar lokitoci a duk fadin kasar Nijar, zai shata wani sabon tsarin inganta aikin jinya tare kuma da daukar matakan gyara kura kurai da ake yi a baya a wannan fannin da nufin ceto rayukan al’umma.

Saurari cikakken rahoton Harouna Mammane Bako

Your browser doesn’t support HTML5

Taron Likitoci a Nijar-3:00"