A cewar kungiyar, har yanzu ba a san adadin mutanen da aka kashe da wadanda suka jikkata ba amma sun baiwa mutane 9 kulawa kafin suka bar garin.
Mutane dubu arba’in ne da suka dogara kan kungiyar agajin a garin Rann domin samun kiwon lafiya.
“Kyale marasa lafiya ciki har da yara 60 da ke cin moriyar shirin samar da abinci ba tare da kulawa ba a wannan sansani, wannan al'amari ne mai ban takaici a garemu.” Inji jami'ar tsare-tsaren gaggawa ta kungiyar a Najeriya, Kerri Ann Kelly.
Ta kara da cewa kungiyar za ta sa ido ta jira da zaran yanayi ya inganta za ta dawo ta ci gaba da aiki.
Shugaba Buhari yayi tir da harin da aka kai inda ya bayyana cewa, “Wadannan hare-haren Boko Haram sun karawa gwamnatinmu karfin kudirin kawo karshen ta’addancin kungiyar a cikin kankanin lokaci. Ina jajantawa Majalisar Dinkin Duniya da sauran kungiyoyin agaji da ke aiki a garin Rann Jihar Borno."
Boko Haram%27s recent cowardly attacks have only renewed the determination of our government to bring the insurgency to a decisive end, in the shortest possible time. I sympathize with the United Nations and other humanitarian agencies working in Rann, Borno State.
— Muhammadu Buhari (@MBuhari) March 2, 2018