Kungiyar Taliban Ta Saki Wasu Fursunoni 'Yan Kasashen Yamma Biyu

Kungiyar Taliban ta saki wasu fursunoni biyu da yammacin yau Talata, don cika alkawarin da su ka yi a yarjajjeniyar musayar fursunoni, wanda ya shafi sakin wasu manyan kwamandojinsu uku.

Majiyoyi masu alaka da kungiyar 'yan ta’addan, sun ce an saki dan Amurka Kevin King da dan Australiya, Timothy Weeks a kudancin lardin Zabul. Da King da Weeks, dukkansu Shehunnan malamai ne a Jami'ar Amurka da ke Kabul, kuma an sace su a watan Agusta 2016 a wajen jami'ar.

Sakin su biyun, ya zo ne 'yan sa'o'i bayan an kai kwamandojin Taliban uku, zuwa Qatar domin musayar fursunonin. Fursunonin kungiyar mayakan su 3, sun hada da Anas Haqqani, wanda babban yayansa ne shugaban ƙungiyar ta’addancin, mai alaka da Taliban, wadda ma, ke amfani da sunanta. Anas Haqqani, tare da kwamandojin Taliban, Haji Mali Khan da Hafiz Rashid, tun a shekarar 2014, gwamnatin Afghanistan ke tsare dasu.